Ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami ya ce ganin damar shugaban kasa ne ya bayyana gaban Majalisa don amsa tambayoyi kan lamuran tsaro.
Malami na magana ne kan amsa gayyatar Majalisar Wakilai da Shugaba Buhari ya yi, don yin bayani kan tabarbarewar tsaro da kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamiala, ya ba da tabbacin amsa gayyatar bayan ganawarsa da Shugaban a fadar Aso Rock.
Kazalika, mai taimakawa shugaban kan labarun yanar gizo Luretta Onochie, ta ba da tabbacin Shugaban zai bayyana gaban hadaddiyar Majalisar Dokokin a yau Alhamis.
Malami ya ce lamuran tsaro da boye bayanan sirri duk suna hannun Shugaban kasa, don haka ba ikon Majalisa ba ne ta gayyace shi ya yi bayani a bainar jama'a kan lamuran tsaro.
Don haka Malami ya ce ganin damar Shugaban ne ya amsa gayyatar ko kuwa ya ki amsawa. Kuma yaki dan zamba ne. Don haka sa Shugaban kasa ya bayyana matakansa gaban Majalisa ba zai zama da alheri ba ganin makiya na iya samun bayanan.
Saurari tattaunawar Umar Farouk Musa da Ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami.
Your browser doesn’t support HTML5