Su dai sarakunan sun kaiwa gwamnan gaisuwar sallah ne, inda suka tabo batun zaman lafiya da kuma matsalolin da ake fama da su a wasu yankunan jihar.
Gwamnan jihar Adamawan da yake karbar manyan sarakunan gargajiyan jihar yace dole a hada hannu wajen ciyar da jihar gaba, musamman a wannan lokaci na matsin tattalin arziki.
Haka nan Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, yace ya zuwa yanzu gwamnatinsa ta kammala gyaran wasu manyan hanyoyin jihar fiye da 46, tare da zuba tubalin fara aikin wasu hanyoyin.
Da ya juya ga batun matsalar rashin biyan albashi da ake fama da shi a yanzu, gwamnan Adamawan yace abun mamaki ne da ma’aikatan jihar ke kuka a yanzu.
Tun farko a jawabansu manyan sarakunan jihar, sun saba layan ganin an samu zaman lafiya a jihar, dake murmurewa daga tashe tashen hankulan Boko Haram.
Da farko dai ga shugaban majalisar sarakunan jihar, mai martaba lamidon Adamawa, Dakta Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha.
Shima a jawabinsa mai martaba sarkin Mubi,yankin da a watannin baya ke hannun yan Boko Haram, Alhaji Abubkar Isa Ahmadu, ya mika kokon baransu ne da a taimakawa al’ummomin da suka noma da takin zamani, tunda yawancinsu manoma ne.
Ba kamar a shekarun baya ba, wannan shekara a jihar Adamawa, an gudanar da shagulgulan sallah ne cikin kwanciyar hankali da lumana, ba tare da fargaba ba.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5