Bayan ya bude jawabinsa da sunan Allah shugaba Buhari yace shi yana son yayi anfani da damar da ya samu ya taya al'ummar kasar murnar barka da sallah.
Yayi fatan Allah ya karbi ibadun bayinsa da addu'o'in da suka yi na watan Ramadan mai albarka.
Shugaban ya sake kira ga jama'a da su yi anfani da nasihohin da aka saurara cikin watan Ramadan "domin kyautata muamala a tsakaninmu" don a so juna a kwatanta gaskiya da rikon amana" inji shi.
Shugaba Buhari ya yi fatan Allah ya sa a yi bukukuwan sallah lafiya, a gama lafiya. Yace a cigaba da sanya kasar cikin addu'a Allah ya kawo karshen duk matsalolin da suka addabeta.
Yace 'Ubangiji Allah ya bamu damina mai albarka. Ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya kara mana arziki a kasarmu. Nagode" inji shugaban.
Ga karin bayani