“Muna wani yanayi ne na gaggawa, ku kasance masu kishi, ku yi wa kasarku hidima domin sadaukarwarku ga kasarku take.” In ji Buhari kamar yadda wata sanarwa dauke da sa hannun hadiminsa Femi Adeshina ta nuna wacce ya sitar a ranar Laraba.
Manyan hafsoshin sojin sun samu jagorancin Ministan tsaro Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya,) wadanda suka hada da Manjo-Janar Leo Irabo wanda shi ne babban hafsan hafsoshin sojin kasar, sai Manjo-Janar I. Attahiru wanda shi ne shugaban dakarun kasa, sai Rear Admiral A.Z Gambo wanda zai jagoranci sojojin ruwa da kuma Air Vice Marshal I.O. Amao, wanda zai jagoranci rundunar sojin sama.
Shugaban na Najeriya ya kuma taya su murna da samun wannan dama, dangane da sassan rundunonin sojin da za su jagoranta.
“Babu wani abu da zan fada muku kan wannan aiki, saboda kuna cikinsa. Ni ma na taba yin sa, zan taya ku da addu’a. Sannan na ba ku tabbacin cewa duk abin da zan iya yi a matsayina na babban kwamandan dakarun Najeriya, zan yi shi, don jama’a su gamsu da ayyukanku.” Buhari ya ce cikin sanarwar.
Ya kuma bukaci manyan hafsoshin da su mayar da hankali wajen karawa manyan jami'ansu da dakarunsu kwarin gwiwa, ya kuma sha alwashin cewa gwamnati “za ta yi iya bakin kokarinta wajen samar da kayan aiki," ga sojojin Najeriya.