Ziyarar kwanaki uku da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ke yi a kasar Netherlands, domin gabatar da jawabi na musamman a wajen bikin cika shekaru 20 da kafa kotun kasa da kasa a birnin Hague, shugaban ya yi ganawa ta musamman da sassa daban-daban na ma’aikatun kasar.
Cikin ganawar da yayi shugaba Buhari ya gana da Fara Minista Mark Rutte, wanda shugaban ya nemi hadin kansa wajen fitowa da tsarin da za a taimaka don farfado da martabar tafkin Chadi da ake kira Lake Chad.
Haka kuma shugabannin biyu sun tattauna yadda za a kawo karshen ta’addancin da ‘yan kungiyar Boko Haram suke yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Fara Minista Mark Rutte, ya amincewa shugaba Buhari cewa kasarsa za ta taimaka wajen bayar da duk gudunmawa da goyon bayan da ake bukata wajen dawowa da tafkin Chadi, wanda ake ganin dauko ruwa daga wasu kasashe na tsakiyar Afirka zuwa tafkin zai taimaka matuka.
Kwararre kan harkar noma Mista AB Sulaiman, wanda yayi wa Muryar Amurka karin haske dangane da alfanu da martabar da za a samu idan wannan tsarin na shugaba Buhari ya samu hadin kan kasar Netherlands.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5