Hukumomin kiwon lafiyar kasar Najeriya sun kira wani taron manema labarai domin yin bayanai akan cutar Ebola da kuma inda aka kwana game da irin kokarin da suke yi na ganin cutar ba ta yadu a kasar ba.
Bayan taron manema labaran, daya daga cikin wakilan Sashen Hausa a birnin Abuja, Madina Dauda ta zauna da ministan lafiyar kasar Najeriya Dakta Halliru Alhassan sun tattauna kan batutuwa da dama masu nasaba da cutar Ebola.
Madina Dauda ta yi mi shi tambayoyi akan ainahin cutar Ebola, ta kuma yi mi shi maganar komawar dalibai karatu a makarantun firamare da na sakandare na gwamnati da masu zaman kan su, sannan kuma ta bukaci ministan yayi bayanin dalilin su na tura wata tawaga kasar Saudiyya a daidai lokacin da aka fara jigilar maniyattan aikin Hajjin bana.
Ga Madina Dauda da Ministan lafiyar Najeriya Dakta Halliru Alhasan kamar yadda suka tattauna:
Your browser doesn’t support HTML5