Kungiyar ta kuma daura damarar daukar matakan da suke fatar zasu samar da mafita daga wadannan matsalolin a lokacin da kungiyoyin suka hadu a Sakkwato dake Arewa maso Yammacin kasar domin daukar matakan.
Lamarin rashin tsaro a Arewacin Najeriya yana ci gaba da karuwa musamman a Jihohin Arewa maso Yamma inda abin har ya kai ga kona mutane da rayukan su har su mutu wanda a kullum kokawa suke yi.
Game da yadda lamarin ke ci gaba da wanzuwa kuma har yanzu matakan da mahukunta ke dauka sun kasa warware matsalolin musamman kisan gilla ga matafiya a Sakkwato yasa gamayyar kungiyoyin ta Arewa suka hadu a jihar don duba yadda zasu fitowa lamarin.
Shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin Arewa Nastura Ashir Shariff ya ce sun fara ne da zaman tattaunawa da wadanda lamarin ya shafa kai tsaye kuma daga cikin abubuwan da suka gano akwai kasawar hukuma tamkar babu gwamnati a kasa. Hakama sun lura da cewa jagororin Arewa basu damu da ganin ci gaban ta ba.
Daidai lokacin da gamayyar kungiyoyin na Arewa ke wannan shirin, tuni wasu jama'a su ka dukufa ga addu'o'i yayinda ita kuwa hukuma ke cewa tana ta kokari duk domin a samu kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5