Asibitoci 45 a jihar Florida da ke kudancin Amurka sun ba da rahoton cewa gadaje sun kare a sashen da ake kula da marasa lafiyan da jikinsu ya yi tsanani.
Hakan na faruwa ne yayin da yaduwar cutar coronavirus ke ci gaba da durkusar da fannin kiwon lafiyar kasar.
Jihar ta Florida, ta ba da rahoton samun karin sama da mutum dubu 12,000 da suka kamu da cutar a jiya Lahadi, rana ta biyar kenan a jere da jihar ke ba da rahoton samun sama da mutum dubu 10 da cutar ta harba a yini daya.
Yankin Miami ya kasance wanda yaduwar cutar ta fi tsanani, inda anan ne tara da daga cikin asibitoci 45 da gadajensu suka kare suke.
A yau Litinin dokar cin tara akan duk wanda ya ki saka takunkumin rufe baki da hanci da Magajin Gari Francis Suarez ya saka za ta fara aiki, inda za a ci tarar duk wanda ya karya dokar a karon dala 50 sannan a ci tarar duk wanda ya sake karya dokar dala 500.