Gaba da gabanta: Shugaban Rasha Ya Gode Ma Amurka Saboda Bayanan Sirri.

  • Ibrahim Garba

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Duk da karce kasar da ake yi tsakanin Amurka da Rasha, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gode ma Amurka saboda bai wa Rasha bayanan sirri masu inganci, wadanda su ka taimaka wajen damko wasu 'yan ta'adda dab da lokacin da su ke harmar kai hari kan wata daddiyar majami'a ta tarihi da wasu wurare masu cinkushe da jama'a.

Fadar Shugaban Rasha ta Kremlin, ta fadi jiya Lahadi cewa hukumar leken asirin tsaro ta Amurka CIA, ta samar da bayanai ga hukumomin Rasha da su ka taimaka wajen dakile jerin shirye-shiryen hare-haren ta’addancin da ISIS ta auna kan birnin St. Petersburg.

Hukumomi a Moscow sun ce Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kira Shugaban Amurka Donald Trump ya gode masa saboda wadannan bayanan da CIA ta bayar, kuma fadar Shugaban Amurka ta White ta tabbatar da kiran da Putin ya yi.

“Saboda bayanan da Amurka ta bayar, hukumomin Rasha sun kai ga kama ‘yan taddan lokacin da su ke dab da kai wani hari wanda idan da ya yiwu da ya kashe mutane da dama,” a cewar Fadar ta White House.

Kasar Rasha ta ce bayanan na da ingancin da har ya kai ga taimaka ma hukumar tsaron kasar wajen bin sawun mutane 7 a makon jiya da su ke shirin kaddamar da hare-hare kan babbar Majami’ar Kazan wadda aka kafa tun karnoni biyu da su ka gabata, da kuma wasu wurare a wannan birnin wanda shi ne na biyu a girma a Rasha. Ko jiya Lahadi ma an sake kama wasu guda uku.