Ga Girki Ga Waka, Sana'a Goma Da Goma

Ina amfani da wakokin wajen mika sako ga ‘yan uwana matasamasamman akan kasancewa masu dogaro da kai, domin itace mafita ga masu zaman kashe wando in ji Bashir Bello, mawaki kuma sana’ar dafa abinci, wanda ake kuma kira da Dan Shila.

Mawaki ya bayyana haka ne a hira da wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir, a birnin Kano.

Ya kara da cewa ya shiga harkar waka ne sanadiyar soyayya inda yarinyar da Allah ya saka masa sonta ke matukar son wakokin Yakubu Muhammad wanda haka yasa ya koyo muryarsa domin ya yi mata waka kuma hakan yasa hakkarsa ta cimma ruwa duk kuwa da cewar soyayyar bata kai su ga aure amma sunyi soyayyar.

Ya kara da cewa bai tsaya ga harkar waka kadai ba domin kuwa yana sana’ar sa ta girki wanda ya samo asali bayan ya sami damar yin aikin abinci a wajen wasu Turawa, da ‘yan India da ma Larabawa abinda yasa masa sha’awar kafa nasa kamfanin na girki.

Ya ce ya fi maida hankali a fannin wakokin soyayya da aure domin a cewarsa da dama akan yi musun cewar tsakanin matar Malam Bahaushe da mijin Bahaushiya wa ya fi dacen aure.

Sannan ya kara da cewa ya kan yi wakokin da suka danganci zaman aure duba da yawa yawan mutuwar aure da ya adabi kasar Hausa.

Your browser doesn’t support HTML5

Girki Da Waka Sana'a Goma Da Goma - 5'06"