Ga Dukan Alama Dubun ‘Yan Boko Haram Ta Kusa Cika

A cikin wani faifan sauti an ji jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau na neman tsari daga Allah bisa irin luguden wuta da ya ce sojojin Najeriya ke yi masu a halin yanzu.

A cikin sautin na minti daya da dakika ashirin da biyu, Abubakar shekau ya yi ta zabga addu"o"i har yake cewa ana cikin watan Ramadan mai alfarma amma ga shi sojojin Najeriya sun tuso su a gaba suna ta azabtar da su.

Ya kuma ce sojojin suna son ganin bayansu, yana mai neman agaji daga Allah mai girma da daukaka. Bayan haka ya nemi jama'a su taimaka masu da addu"o’i, daga karshe an ji Shekau ya fashe da kuka.

Kanar Sagir Musa, kakakin rundunar sojan Najeriya, ya ce akwai kanshin gaskiya a wannan batu amma ba za su bata lokacinsu wajen tantance sautin ba saboda su dai kokarinsu shi ne su kawo karshen duk yan ta'adda a arewa maso gabas da ma zirin tafkin Chadi.

Masani kan kungiyoyin ‘yan ta'adda, Farfesa Mohammed Tukur Baba, ya ce wannan abu na nuna cewa karshen kungiyar ne yazo ganin ko a kwanakin baya ma sai da aka ruwaito sun fara neman sabbin mayaka, musamman duba da cewa mayakan sun gaji da yakin tunda duk wasu dabarunsu sun kare.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Ga Dukan Alama Dubun ‘Yan Boko Haram Ta Kusa Cika