Furucin Trump Cewa Kungiyar NATO Ta Tsufa Tamkar Cina Mata da Amurka Wuta Ne -Farfasa Alhassan

Angela Merkel shugabar kasar Jamus da Donald Trump shugaban Amurka dake jiran gado.

Cikin maganganun da Donald Trump yake tayi tun kafin a rantsar dashi shugaban Amurka yace kungiyar NATO ta tsufa lamarin da yanzu ya tada hankulan shugabannin kasashen turai da tsoffin jakadun Amurka da ma 'yan jam'iyyarsa ta Republican

A zantawar da Muryar Amurka tayi da Farfasa Yusuf Alhassan na Jami'ar Kansas dake nan Amurka yace furucin na Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado, kamar ya cinawa dangantakar kasashen turai da ita Amurka wuta ne.

Amurka ita ce ran NATO kuma su kasashen yammacin turai su ne suke marawa Amurka baya walau ana batun yaki ne ko shirin tattalin arziki. Inji Farfasa Alhassan idan yau babu NATO, ke nan babu wannan dangantakar.

Yace muddin Trump ya wargaza NATO abubuwa ne barkatai zasu faru. Da Trump yace kungiyar ta tsufa da sai ya bayyana irin garambawul da yakamata a yi mata, amma bai yi ba. Dalili ke nan shugabar Jamus Angela Merkel ta fito nan da nan ta mayar masa da martani.Tace har yanzu babu wata kungiya da ta kai karfin NATO tsakanin Amurka da kasashen Tarayyar Turai.

Goyon bayan kalamun Trump da shugaban Rasha Vladimir Putin yayi, yana son NATO ta wargaje kamar yadda tasu kungiyar USSR ta wargaje, wato a taru a yi mutuwar kasko.

Ga karin bayani daga firar da Farfasa Alhassan.

Your browser doesn’t support HTML5

Furucin Trump Cewa Kungiyar NATO Ta Tsufa Tamkar Cina Mata da Amurka Wuta Ne -Farfasa Alhassan - 6' 08"