Fursunoni 40 Suka Halaka A Fadacefadacen Da Barke A Kasar Brazil

Yansanda A Kofar Kurkukun Brazil

Gidajen kurkukun kasar Brazil sun tabbatar da cewa fursunoni akalla 40 aka hallaka a sanadin fadacefadacen da suka barke.

Hukumomin gidajen kurkukun kasar Brazil sun tabbatar da cewa fursunoni akalla 40 aka hallaka a sanadin fadacefadacen da suka barke a wasu gidajen yari 4 dake jihar Amazonas dake arewancin kasar jiya Litinin, wanda akace fadan na da alaka da kungiyoyin ‘yan bata-gari.

Duk gidajen yarin suna babban birnin jihar Manaus, inda aka kashe mutane 15 lokacin fadan tsakanin ‘yan kugiyoyi biyu, a gidan yari na 5.

Hukumomi sunce mutanen da aka kasha jiya Litinin, an kasha su ne ta hanyar shake su.

Gwamnan jihar Amazon Wilson Lima yace ministan shari’a Serigio Moro zai kaddamar da kwamitin bincike akan aukuwar lamarin.

Fadan kungiyanci ba bakon abu bane a gidajen yarin Brazil da suke makil da jama’a, musamman a tsakanin ‘yan kungiyoyi masu alaka da abubuwan sha masu sa maye. Fiye da mutane 100 aka yima yankan rago lokacin wani fada da ya barke a gidajen yarin Brazil a shekarar 2017.