Furodusa Abubakar Maishadda Na Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Abubakar Bashir Maishadda (Instagram/Ali Nuhu/Kibadash photos)

Kamfaninsa ya samar da fina-finai irinsu Sarki Goma Zamani Goma, Hauwa Kulu, Mariya, Wutar Kara, Hafeez, Mujadala, Ana Dara Ga Dare da dai sauransu.

Fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood da ke Najeriya, Abubakar Bashir Maishadda na murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Tauraron fina-finan Hausa Ali Nuhu ne ya wallafa a shafinsa na Instagram inda yake taya Maishadda murnar zagayowar wannan rana.

Maishadda wanda shi ya kafa kamfanin Maishadda Global Resources ya hada manyan fina-finan Hausa da suka yi fice tare da samun karbuwa a wajen masu sha’awar kallon fina-finan Hausa.

Kamfaninsa ya samar da manyan fina-finai irinsu Tsakaninmu, Sarki Goma Zamani Goma, Hauwa Kulu, Mariya, Wutar Kara, Hafeez, Mujadala, Ana Dara Ga Dare da dai sauransu.

A halin da ake ciki kamfanin na shirin fara daukan wani fim sabo mai dogon zango mai suna “Bintu,” kamar yadda Ali Nuhu ya bayyana.

Ya kuma saka manyan taurarin Kannywood irinsu Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Abba Al Mustapha, Falalu Dorayi, Maryam Yahaya, Rahama Sauda, Mommy Gombe, Yakubu Muhammed, Umar M. Shariff da sauransu a fina-finansa.