A bayanan da suka bayar a yayin wani taron manema labarai da suka kira a birnin Yammai, shugabannan al’ummar Fulani makiyaya a arewacin Tilabery sun bayyana koken su akan azabar da suka ce suna fuskanta daga wasu ‘yan bindiga dake karkashin umurnin Janar Gamo, wani kwamandan kungiyar ‘yan tawaye dake sintiri akan iyakar Nijar da kasar Mali, da nufin farautar masu tayar da kayar baya.
Bubakar Abdullahi shine shugaban kungiyar makiyayan arewacin Tilabery, ya ce makiya na cikin mawuyacin hali, ana korarsu, a hana dabbobinsu shan ruwa, ko kiwo, ana kuma yi masu sata ko ma a kashesu (fulanin).
Yanayin da ake ciki a yau a arewacin Tilabery, Fulani makiyaya sun zama tamkar mujiya a cikin dangi inji su. Inda ake hallaka mutanensu ba kakkautawa saboda zargin aikata ta’addanci, duk da cewa ba su da alaka da wata kungiyar tayar da kayar baya. Bukar Abdullahi ya kuma ce, ce ya kamata a daina irin wannan kazahin.
Halin zaman doya da manja tsakanin buzaye da makiyaya a arewacin Tilabery da aka shiga a yau ya tilastawa Fulani makiyaya ficewa daga daji domin tarewa a birane a cewar Jibbe Mammane, mazaunin kauyen Gumbi.
Sakamakon lura da yadda lamuran tsaro ke kara tabarbarewa akan iyakar Mali da Nijar ya sa majalisar dokokin Nijar gayyatar ministan tsaro Kalla Moutari ya hallara a gaban wakilan al’umma a karshen makon jiya, domin yin bayani akan wannan batu. Kodayake ministan ya amsa wannan kiran, a karshe an dage zaman tattaunawa zuwa gaba ta yadda za a fassara masa bayanan da dan majalisa Karimu Burema yayi. dangane da abinda ke faruwa a wannan yankin.
Fada a tsakanin Fulani da buzaye wani abu ne da ya zama ruwan dare yanzu a kauyukan Tilabery masu makwabtaka da iyakar kasar Mali. Na baya bayan nan shine wanda ya faru a wasu zanguna a karkashen makon jiya inda rahotanni ke cewa mutane dayawa sun mutu a sanadiyar wannan artabun.
Gwamnatin Nijar a farkon makon da ya gabata ta aike da ministan cikin gida Bazum Muhammed zuwa karkarar Kurfei domin gargadin jama’a su zauna lafiya da juna.
Your browser doesn’t support HTML5