Wannan na kunshe a wata takardar koke da ‘yanuwan mamatan suka gabatarwa kwamishinan ‘yansanda na jihar Adamawa Mal. Musa Kimo dauke da hotunan matasan lokacin da suke raye a caji ofis na Kiri da kuma na gawarwakinsu da aka yiwa daurin goro kwance kan uwar madatsar ruwa na Kiri.
Mahaifan wadanda aka kashe Mal. Kunuri Hampeto da Alhaji Bakari Kem sun shaidawa Muryar Amurka cewa bayaga gallazawa da barazana ga rayuwarsu lokacin da suka nemi DPO ya yi masu bayanin inda ‘ya’yansu suke, ya tozartasu biyan taran kudi sama da naira dubu dari shida da kuma shanu.
Mori Ori daya daga cikin wadanda suka sallake rijiya da baya da yanzu ke zaman gudun hijira na sama da watanni shida ya yi bayanin yadda ya kubuta ‘yan sa’o’i kamin ‘yan bangan Talum da DPO ya mika a hannunsu su kashe shi.
Lauya mai bi wa makiyayan hakkinsu Barr, Abubakar Kolone ya ce suna tuhumar harbe Ardo Kiri babban shaida da suke dashi a tuhumar da suke yi wa DPO Dass da wani dan bindiga da ba a san ko wanene ba mako daya bayan kashe samarin nan hudu yana kama da wani yunkuri na yin rufa-rufa game da korafinsu.
Wakilinmu Sanusi Adamu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Othman Abubakar wanda ya tabbatar da abkuwar al’amarin ya ce rundunar ta sauyawa jami’inta da ake zargi wurin aiki zuwa shelkwatanta domin tabbatar da adalci wurin kaddamar da bincike mai zurfi kan korafin da makiyayan suka gabatar.
Kisan matasan hudu na zuwa ne sakamakon tuhumar da ‘yan sanda ke yi masu na kisan tsohon kantoman yankin na Kiri Alhaji Gambo a watan Afrilun shekarar 2016.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5