Shugabar FOMWAN ta kasa, Rafiatu Idowu Sani ce ta yi wannan kira a wani taron manema labarai da ta kira a Abuja.
Saidai ga mai fashin baki a al'amuran tsaro na ganin akwai sakacin hukuma.
Shugabar Kungiyar FOMWAN ta kasa Hajiya Rafi'atu Idowu Sani ta bayyana takaicin kungiyar a game da ta6ar6arewar harkar tsaro a kasar, lamarin da ke cigaba da haifar da hasarar rayukan al'umma babu ji babu gani.
Rafi'a ta ce tun ana bin mutane a manya tituna kasar, yanzu gida gida ake bi ana kama maza da mata ana kashe su ana kuma garkuwa da su har bayan sun kar6i makudan kudade daga hannun dangin wadanda suka kama.
Rafi'a ta yi Allah wadai da yadda al'amarin zai iya shafa harkar ilimi musamman a shiyoyin Arewa, inda matsalar ta fi kamari.
Rafi'a ta ce dalibai a makarantu ma ba su tsira ba. domin sace su da ake yi yana rage kwarin gwiwar yara wajen komawa makaranta musamman ma dalibai mata lamarin da ba zai ta6a sa6uwa ba.
Rafi'a ta ce ya kamata Gwamnati ta aiwatar da hakkin da ya rataya a wuyarta kamar yadda Kundin tsarin mulki ya tanada, na kare rayuka da dukiyoyin al'umma kuma ta na so Gwamnati ta yi shi a zahirance.
Daya daga cikin Jami'an Kungiyar, Farida Sada ta ce kungiyar na bada shawara ga Gwamnati da ta yi ho66asa wajen tuntu6ar Sarakuna, Shugabanin Kasa, Gwamnoni, Shugabanin Kanana Hukumomi, Mata da Matasa domin samun bakin zaren.
Kungiyar ta ce Gwamnati tana kashe kudi wajin magance harkar tsaron amma ga duka alamu kokarin na Gwamnati ba ta yi wani tasiri ba ganin yadda sace sacen mutane da yin garkuwa da su karuwa ya ke yi kullum.
Ga mai fashin baki a al'amuran tsaro, Dr Yahuza Getso, ya yi tsokaci akan batun yana mai cewa akwai sakacin hukuma, domin akwai tabbacin ana kashe makudan kudade amma me ke faruwa da ba a samun nasara yadda ya kamata? Yahuza ya ce akwai abin dubawa a bangaren da ke kula da bayanan sirri, saboda ya kamata a yi amfani da hanyoyin zamani wajen gano inda miyagun suke a 6oye, kuma a dauki mataki akansu. saboda a shawo kan ta'addanci da sace sacen mutane.
Kungiyar FOMWAN ta ce tana mai bada shawara ga Gwamnati da ta dauki matakan sulhu maimakon yin amfani da karfin soji.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5