A shekarar 2002 ne Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar tayar da kungiyoyi da gwamnatoci daga bacci akan bukatar karfafa ayyukan ganar da jamaa illolin dabiar bautar da yara, yanzu haka yara miliyan 152 ne ke fama da wannan matsala dalilio kenan da aka karkatar da shagulgulan ranar ta bana ga ayyukan wayar da kai akan bukatar kula da lafiyar yara tare da karesu daga hadarin da ke da nasaba da dalilan aiki.
Nijar na daga cikin kasashen da suka dade da amincewa akan maganar yaki da bautar da yara kokuma sanya yara aikin da yafi karfin su, alamu na nuna cewa haryanzu akwai sauran aiki, dalili kenan da kungiyoyi irin su ALTEN suka fara yunkurin ankarar da gwamnatin kasar abubuwan da ke faruwa dan ganin an fito da wasu sabbin dabaru.
kungiyar kwatago ta duniya ta sanar cewa nahiyar Afrika ce kan gaban yankunan da aka fi bautar da yara a duniya yayin da aka gano cewa daga cikin miliyan 152 da ke cikin wannan hali, kashi 70.9 na aiki a fannin noma sai kuma fannin masana'antun dake bautar da kashi 11.9 yayin da kashi 17.2 suke cikin wani hali a ma'aikatun bariki .
Ga Rahoton Sule Mummuni Barma
Your browser doesn’t support HTML5