Fiye Da Mutum 40,000 Suka Kamu da Cutar COVID-19 a Rana guda a Amurka

Kasar Amurka ta kara samun adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar coronavirus a duk rana, adadin da ya zarta 40,000 a karon farko.

Rahoton jaridar Washington Post ya nuna cewa sabon adadin masu kamuwa da cutar a rana a Amurka ya wuce wanda aka sanar ranar Alhamis 25 ga watan Yuni inda jihohi 5 suka sanar da adadi mafi yawa a rana guda, wato jihohin Florida, South Carolina, Georgia, Tennessee da Utah.

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence

A lokacin wani taron manema labarai tare da kwamitin da ke sa ido kan cutar coronavirus a fadar White House, mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence ya fadi cewa jihohin kasar 16 na fuskantar karuwar masu kamuwa da cutar kuma a kwanan nan jihohi 34 sun bayyana cewa adadinsu ba ya karuwa sosai.