Fitaccen Dan Wasan Fina Finai Sadiq Daba Ya Rasu

Sadiq Abubakar Daba

Sadiq Abubakar Daba, wanda aka fi sani da Sadiq Daba ya rasu da misalin karfe takwas da rabi na yamma bayan ya yi fama da rashin lafiya na lokaci mai tsawo.

Sadiq Daba, wanda dan asalin jihar Kano ne, ya girma a kasar Saliyo, ya kuma dawo Najeriya ya bar iyayensa da sauran ‘yan’uwansa a Saliyo yana da shekaru kusan ishirin.

Ilimi

Sadiq Daba ya yi makarantar firamare a kasar Saliyo. Bayan dawowar shi Najeriya ya tafi makarantar koyon aikin talabijin ta kasa da ake kira NTA/TV College a Jos. Ya karo karatu a makarantu da dama da suka hada da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria inda ya sami digiri na biyu, Ya kuma yi kosa kosan aikin sadarwa a kasashen waje.

Marigayi Daba ya sha bayyana cewa ya fara sha’awar radiyo tun yana karami a kasar Saliyo, inda ya tashi yana sauraron radiyo yana kuma kwaikwayon yin magana a radiyo a gaban madubi a gidan su.

Aikin da ya yi

Sadiq Daba ya yi aiki a wurare da dama kafin burin sa na aikin jarida ya cika lokacin da ya nemi aiki a gidan Radiyo da Talabijin na Kaduna da ake kira RKTV. Ya kuma yi aiki a tashar talabijin ta kasa NTA Sokoto, da a lokacin ake kira NTV, ya yi aiki da NTPC Lagos, da kuma NTA Lagos. Ya kuma rika gabatar da wani shirin talabijin da ya ke shiryawa da kansa a tashar DTN da ake kira “Sadiq Daba presents.”

Wasannin fina finai

Tauraron Sadiq Daba ya fara haskawa ne a shekarar 1970 lokacin da ya fito a wani wassan kwaikwayo na tashar NTA da ake kira "Cockcrow at Dawn" da ya fito da suna "Bitrus". Sadiq Daba ya sami lambar yabo a shekarar 2015 ta gwanin wasannin fina finan Afrika, da ya fito a matsayin "Inspector Waziri” a wasan da aka ba labaki "October 1", wanda yanzu haka ake nuna wa a tashar fina finai ta NETFLIX. Ya kuma fito a wani wasan kwaikwayo da ake kira "Citation" wanda shi ma ya sami karbuwa ainun. Wasannin kwaikwayon talabijin da ya fito sun hada da "Behind the Clouds’, "A Place Like Home", "Soweto", da "Moment of Truth".

A shekara ta 2017, bayan ya dade yana fama da rashin lafiya, an yi wani kwarya-kwaryan neman tallafin kudin domin kai shi asibiti, lokacin da aka ji cewa, yana bukatar sama da Naira miliyan tara domin jinya.

Sadiq Daba ya yi rubutu na karshe a shafinsa na twitter ranar daya ga watan Janairu 2016 inda ya bayyana cewa bai iya barci ba da dare sabili da matsanancin ciwon ciki.

Sadiq Daba ya rasu ya bar matarsa Bokaji Daba da suka hadu suka kuma yi aure a Jos, yaya da kuma jikoki.

Tuni ma'abota mamacin suka fara wallafa sakonnin ta'aziya a shafukansu na sada zumunta.

Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya kuma fitaccen mawallafin mujalla Dele Momodu ya bayyana jimaminsa dangane da rasuwar Sadiq Daba


Shi ma wani bature da ya ke kiran kansa Dan Najeriya farin fata "White Nigerian" ya wallafa sakon ta'aziya a shafinsa.

Karin bayani akan: jihar Kano, NTV​, Sadiq Daba, Nigeria, da Najeriya.