Firayim Ministan Israila Zai Janye Daga Yarjejeniya Akan 'Yan Gudun Hijiran Afirka

Firayim Minista Benjamin Netanyahu yayinda yake bayyana matsayinsa akan 'yan gudun hijira daga nahiyar Afirka

Yarjejeniyar da Israila ke son ficewa daga ciki ta tanadi ci gaba da rike 'yan gudun hijiran Afirka 16,250 har zuwa lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta samar masu wurare a nahiyar Turai a ksashe kamar Jamus, Italiya da dai sauransu

Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, jiya Litinin ya bada sanarwar zai jingine yarjejeniyar da Bani yahudun ta cimma da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD na sake tsugunar da dubban 'yan ci rani daga Afirka a wasu kasashen yammacin duniya.

Sa'o'i bayan ya bada sanarwa kan wannan yarjejeniya, Mr. Netanyahu ya bayyana ta shafinsa a Facebook cewa, zai jingine yin aiki da shirin sai bayan an sake gudanar da wani nazari.

Karkashin yarjejeniyar, 'yan gudun hijirar, wadanda suka ce suna neman mafakar siyasa, amma da Isra'ila take kallaonsu a zaman 'yan ci rani, dubu 16, 250 za'a sake tsugunar dasu a kasashen Canada,da Italiya, da Jamus, kamar yadda Firayim Ministan yayi bayani a jiya Litinin. Yayinda aka kai wannan adadi kuma za'a basu izinin ci gaba da zama a Isra'ila.

Amma jim kadan bayan bada wannan sanarwa wadannan kasashen yammacin duniya kama daga Jamus suka ce basu da masaniya gameda wannan yarjejeniyar.

Galibin wadannan 'yan gudun hijiran sun fito ne daga kasashen Eritrea, da kuma Sudan wacce take fama da yake yake.