Ga dukkan alamu, hadakar jami’yun siyasar da malamin Shi’an nan mai yawan sukan Amurka, Muqtada al Sadr, ta doshi samun nasara a zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a Iraqi.
Yayin da aka kusan kammala kidayar dukkanin kuri’un, gamarrayar jam’iyyun mai hankoron ganin an samar da sauyi ta al -Sadr, na kan gaba da yawan kuri’a a yankuna shida, yayin da kungiyar da kwamandan mayakan sa-kai ta Iraqi, Hadi al - Amiri ke biye da ita a yawan kuri’u.
Firayi Minista Haider al Abadi da ke kan mulki, wanda kuma ke samun goyon bayan Amurka, na biye da abokanan hamayyarsa, inda kuma ya kira ‘yan kasar ta Iraqi da su amince da sakamakon zaben da za a fitar.
Daruruwan magoya bayan, al-Sadr, sun yi ta nuna farin cikinsu a kan titunan birnin Bagadaza yayin da aka bayyana wani kashi na sakamakon zaben da aka yi.
Wasu dai na kwatanta wannan al’amari a matsayin sabon babi a rayuwar jama’ar kasar ta Iraqi” yayin da wasu ke bayyana shi a matsayin “karshen badakalar cin hanci da rashawa.”