Daruruwan magoya bayan malamin nan na ‘yan Shiite Muqtada Al-Sadr ne suka hau titi da daren jiya Lahadi suna zanga-zangar nuna jin dadin nasarar da gwanin nasu yayi a sakamakon zaben ‘yan majilisar dokokin kasar da aka fara fitar wa na zaben da akayi.
Hukumar zaben kasar tace yanzu haka dai Al-Sadr shine ke kan gaba a ciki ‘yan takarar zaben kasar da aka gudanar, domin ko sakamakon da aka fara fitarwa na sama da rabi ya nuna cewa shine ya lashe a kussan dukkan gundumomi.
Wanda ko yazo na biyu shine wanda yayi kawance da sauran jamiyyu.
Nasarar Al-Sadr zai zamo wani babban koma baya ga sake zaben Prime minister Haider Al-Abadi.
Yanzu dai in har ta tabbata cewa Al-Sadr shine yayi nasarar to dama dai shi ba boyayye bane wajen sukan manufar Amurka, wanda hakan kuma zaiyi tasirri wajen tabbatar da wanene zai zamo shugaban kasar tasu.
Daga lokacin zaben dai kawo yanzu ana sa ran a fidda daukacin sakamakon zaben a ciki kwanaki biyu na kujeru 329.
Facebook Forum