Firai Ministan kasar Turkiya ya yi kira ga Shugaban kasar Masar ya saurarin godon al'ummar kasar

Dandazon masu zanga zanga a dandalin 'yanci na Birnin Alkahira, Masar, Fab.1, 2011

PM kasar Turkiya ya yi kira ga shugaban kasar Masar Hosni Mubarak dake fuskantar matsin lamba, da ya biya bukatar mutanenshi

Firai Ministan kasar Turkiya ya yi kira ga shugaban kasar Masar Hosni Mubarak dake fuskantar matsin lamba, da ya biya bukatar mutanenshi, yayinda suke ci gaba da zanga zangar neman canji. A cikin jawabinsa ga majalisar dokokin kasar Turkiya, Firai Minista Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Mr. Mubarak ya saurari godon mutanen. A halin da ake ciki kuma, babban jami’in kare hakin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yau Talata cewa, gwamnatin Mr. Mubarak tayi mummunan keta hakin bil’adama da suka hada da azabtaswa. Jiya Litinin Amurka ta kushewa yunkurin kafa sabuwar gwamnati da Mr. Mubarak ya yi da cewa, lamarin yana bukatar daukar mataki ba zabar mutane su rike mukamai ba. Kasashen ketare suna ci gaba da yunkurin kwashe mutanensu daga kasar Masar yau Talata yayinda zanga zanga take kara kamari a kasar ta Larabawa. Amurka tace tana kokarin kwashe wasu Karin Amurkawa dubu daya da dari hudu a cikin kwanaki masu zuwa bayan ta kwashe sama da mutane dubu da dari biyu. Gwamnatin Amurka tayi shatar jirage tara da zasu kwashe mutane daga kasar Masar zuwa Turkiya da Cyprus da kuma Girka. Jami’ai a Turkiya da kuma Cyprus sun ce suna shirye shiryen gaggawa na tsugunar da ‘yan yawon bude ido da za a kwashe daga Masar da kuma ganin sun isa inda zasu je cikin sauri.