Firai Minista Modi Ya Kare Sabuwar Dokar Zama Dan Kasa A Indiya

Firai Ministan Indiya Narendra Modi

Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya maida martanin kariya a kan da’awar da masu sukar sabuwar dokar zama dan kasa da suke zargin nuna wariya ne ga Musulmai, a wani gangamin yakin neman zabe a New Delhi, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga a kasar.

Modi yana jawabi ne a taron kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar sa ta BJM na zaben majalisar dokoki da za’a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa, yayin da kai tsaye ya dauko zancen dokar mai cike da cece-kuce.

“Majalisar wakilai da kuma dattawa, da ma dukkan daukacin ‘yan majalisa sun ba da gudummuwa wajen tabbatar da wannan doka domin kyautata rayuwar jama’ar kananan kabilu, da kuma wadanda aka ci zarafinsu.

“Ya kamata ku girmama majalisar dokokin kasar ku, ku kuma girmama ‘yan majalisun da jama’a suka zaba”, a cewar Firai Minista Modi.

Fiye da mutane 20 ne suka rasa rayukan su a fadin kasar, a arangama da ‘yan sanda, tun sa’adda majalisar dokoki ta zartar da dokar mai cike da wariya da nuna bambancin a farkon watan Disamba 2019.

Dokar za ta bada dama ga mabiya addinin Hindu, da Kiristoci, da ma wasu addinai marasa rinjaye da suka shiga kasar a ta haramtacciyar hanya, da su kasance ‘yan kasa, idan har zasu iya tabbatar da cewa an gallaza musu akan bambancin addini, a kasashen da ke da rinjayen Musulmai kamar Bangladesh, Pakistan da Afghanistan.

Sai dai sabuwar dokar bata hada da Musulmai ba marasa rinjaye a kasar.