Fim din shahararren jarumin nan na Bollywood, Shah Rukh Khan, da Anushka Sharma, mai suna Jab Harry Met Sejal, da aka dade ana jira ya fito yau juma’a, a kasar Indiya, ana kuma sa ran cewa wannan fim din zai fito da sa’a domin ana harsashen cewa zai baiwa marada kunya .
Ana sa ran cewa a ranar farko fim din zai yi cikin fiye da dalar Amurka miliyan uku, hatta masu fashin baki akan harkokin kasuwanci a Indiya, kamar Akshaye Rathi, ya tabbatar da cewar daga dukkan alamu fim din zai yin kasuwan da ake zato.
Ya kara da cewa a ranar farko yana harsashen cewa gidajen kallo a kasar zasu cika makil masamman ma na birane wanda dama su ake hako.
Ganin cewa akwai fiye da gidajen kallo dubu uku (3,000) da za a iya amfani dasu domin gamsar da masu kallo haka shima zai taimaka wajan samun Karin kudaden shiga.
Your browser doesn’t support HTML5