A ranar Lahadi 10 ga watan Maris ne aka yi bikin karrama wasu fitattun 'yan wasan fina-finai da suka taka rawar gani da lambar yabon Oscars ta shekarar 2024.
Da'Vine Joy Randolph, na daga cikin wadanda suka lashe lambar yabon Oscars a shekarar 2024 a daren Lahadi, nasarar da aka yi ta hasashe a kai.
Fim din 'Oppenheimer' ne aka fi zaɓa a wannan shekarar, wanda ya mamaye 7 daga cikin rukunonin da ya yi takarar da su, ciki har da Mafi kyawun Hoto da Babban Darakta.
A rukunin fitaccen fim mai ba da labari na kasa-da-kasa, an zabi fim din “I.O Capitano,” wanda mai ba da umarnin nan dan kasar Italiya Matteo Garrone ya hada, a takarar lashe lambar yabon, sai dai “The Zone of Interest” na kasar Burtaniyya ne ya lashe wannan rukunin.
Fim din na "I.O Capitano' ya bibiyi labarin wani karamin yaro ne, wanda ya bi ayarin bakin haure daga Senegal ya ratsa ta hamada a Nijar zuwa Libya, inda suka shiga wani kwale-kwalen ‘yan fasa-kwauri da ke makare da bakin haure.
Ga jerin wasu da suka yi nasara a bikin gasar Oscars ta ranar Lahadi:
BEST PICTURE
“Oppenheimer”
BEST ACTRESS
Emma Stone, “Poor Things”
BEST ACTOR
Cillian Murphy, “Oppenheimer”
SUPPORTING ACTOR
Robert Downey Jr., “Oppenheimer”
DIRECTOR
Christopher Nolan, “Oppenheimer”
“Oppenheimer,” Ludwig Göransson
FILM EDITING
“Oppenheimer,” Jennifer Lame
CINEMATOGRAPHY
“Oppenheimer,” Hoyte Van Hoytema
INTERNATIONAL FEATURE FILM
“The Zone of Interest” (United Kingdom)