Da yake zantawa da manema labarai a bikin ranar dimokaradiyya da cika shekaru biyu akan mulki, gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya ce suna da yakinin sake gina kasuwar ta Jos da ta kone shekaru 15 da suka gabata, wanda hakan zai inganta harkokin kasuwanci a jihar.
A cewar gwamnan lokacin da suke yakin neman zabe sunyi alkawarin sake gina kasuwar, wanda hakan yasa yanzu suka samar da kwamitin da zasu gudanar da aikin. Haka kuma gwamnan yayi kira ga ‘yan kasuwa da su saka hannu domin taimakawa gwamnati.
Albarkacin ranar tunawa da dimokaradiyya gwamnan jihar Filato ya yiwa wasu firsinoni shida afuwa, kamar yadda Kwamishinan Shari’a a jihar Filato Jonathan Mawiyau, ya tabbatar.
Shugaban kungiyar kwararru a harkar yada labarai reshen jihar Filato, Nde Gideon Barde, ya shawarci gwamnatin jihar Filato da ta mayar da hankali ga kyautata aikin gona da kuma ilmi domin samun ci gaba.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5