Matakin da gwamnatin Jihar Nasarawa ta dauka na rufe makarantun sakandare da firamare a Jahar ya sanya al’ummar Jahar yin kira wa gwamnati kan ta dauki matakan tsaro don baiwa dalibai damar samun ilimi.
Rufe makarantun ya zo ne a dai-dai lokacin da dalibai ke rubuta jarrabawa ta kasa da zai basu guraben shiga manyan makarantu.
Wani dake zaune a kan iyakar Abuja, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida cewa rufe makarantun zai shafi harkar ilimi a Najeriya.
Honarabul Hafsat Abdullahi, wata uwa daga Jihar Nasarawa, ta ce matakin da hukumomi suka dauka na sallamar yara daga makarantun ya yi dai-dai saboda sai da lafiya ilimin zai samu.
Shiko Alhaji Garba ‘Dan Malam daga garin Keffi a Jihar Nasarawa ya ce tun farko sakacin gwamnati ne ya kawo ga halin da al’umma ke ciki, don haka ya ce dole a dauki matakan gyara.
Komishiniyar Ilimi a Jihar Nasarawa, Hajiya Fati Jimeta Sabo ta ce gwamnatin jihar ta Nasarawa ta rufe makarantun ne don kariya kan lamarin rashin tsaro a Abuja dake makwabtaka da jihar.
A halin da ake ciki dai, daukacin makarantun gwamnati da masu zaman kansu da jami’o’i da wassu manyan makarantun jihar zasu kasance a rufe har sai lamura sun daidaita.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5