Hukumar FIGC ta dauki wannan mataki ne don tantance ko zata bukaci janye hukuncin da ta yanke a wannan shekara, lokacin da kotun tarayya mai kula da sha’anin wasanni ta wanke Juventus da wasu kungiyoyi 10 a kan lissafin kazamin riba da suka samu a kasuwar musayar ‘yan wasa.
Lauyoyim Turin sun fada a ranar Litinin cewa sun kammala bincike a kan yadda kungiyar Juventus ta gudanar da harkokin kudinta tsakanin shekarar 2018 da 2020, yayin da suka kuma gudanar da bincike a kan zargin karya a lissafi da magudi a kasuwar ‘yan wasa da aka yiwa fitacciyar kungiyar ta Serie A.
Juventus, da kasuwar zuba hannun jari ta Milan ta ayyana a matsayin kulob din Italiya da ya yi fice, ya musunta duk wani zargin aikata ba daidai ba, yana mai cewa ya bi duk wata ka’ida daidai.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a makon nan, babbar mai shigar da kara a birnin Turin, Anna Maria Loreto, ta ce an sanar da kungiyar Juventus da hukumarta da manyan jami'an hukumar binciken sha’anin kudinta cewa an kawo karshen binciken da ake yi a yanzu.