Hukumar kwallon kafar duniya wato FIFA, ta samar da karin wa’adin kammala wasannin neman gurbin gasannin kwallon kafa na cin kofin nahiyar Afirka da kuma na duniya a shekara mai zuwa.
Hukumar ta FIFA ta shata wa’adin watanni hudu na Maris, Agusta/Satumba, Oktoba da Nuwamban shekarar ta badi ga nahiyar ta Afirka domin karasa wasannin na neman gurbi, wanda ya ba da adadin wasanni 12 da kowace kasa za ta iya bugawa, idan har akwai yanayin tsaron lafiyar jama’a.
Da ma can kasashen na Afirka su na bukatar ranakun buga wasannin 12 ne domin su kammala wasannin na neman gurbi, inda suke bukatar wasanni 4 na neman gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da kuma 8 na gasar cin kofin duniya.
An dage fafata gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka tsara yi a shekarar 2021 a Kamaru zuwa watannin Janairu da Fabrarun shekara ta 2022, a yayin da kuma za’a iya yin amfani da hutun watannin Maris da Yuni domin kammala wasannin neman gurbi.