FIFA Ta Dakatar Da Ugo Njoku

Kwallon mata

Hukumar Kwallon kafa ta FIFA ta dakatar da 'yar tsaron gida ta Super Falcons Ugo Njoku har na tsawon wasanni uku da zasu buga nan gaba a sakamakon wani wasan keta da tayi.

An kuma caji 'yar wasan da biyan kudi kwatan kwacin dala 3200 a sakamakon samun ta da laifin karya dokar hukumar ta FIFA.

Kamitin horaswa na FIFA ya tsaida shawarar ne bayan gano cewar 'yar wasan ta yi anfani da gwiwar hannu da yin keta a yayin da suke fafatawa da tsakanin su da 'yan wasan Australiya a wasan cin kofin duniya na mata da ake gudanarwa.

Njoku baza ta buga wasan karshe na rukunin da Super Falcons za su buga da Amurka gobe Talata in Allah ya kaimu ba. Ragowar wasannin kuwa sun ta'allaka ne akan in har Najeriya ta ci wasan ta na gobe.

Kungiyar Falcons na bukatar maki uku ne kacal a wasan da za su buga da Amurka idan har suna son su wuce zuwa wasan kwata final.