Kwararren likitan nan na Amurka a fannin cututtukan da ke yaduwa Anthony Fauci, ya fada a jiya Talata cewa adadin mace-macen da aka samu a Amurka kusan ya fi mutum dubu 81 da aka ba da rahoton akai.
Ya yi gargadin cewa akwai sakamako mai tsanani idan birane da jihohi suka bude harkokinsu cikin sauri.
Fauci ya fada wa wani kwamitin majalisar dattawa da ke bincike akan yadda Amurka ke daukar matakai game da annobar cewa akwai mutane da yawa da suka kamu da cutar coronavirus da ba a sani ba.
Ya kara da cewa musamman a birnin New York, mutane da dama sun mutu a gidajensu ba tare da an sanya sunayensu a kundin mace-mace na kasar ba a hukumance.
Sai dai Fauci ya ki ya yi hasashen adadin mutanen.
Fauci ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar annobar za ta iya tsananta a Amurka daga watan Satumba zuwa Nuwamba, amma dai ya ce yana fatan a lokacin kasar za ta tunkari annobar fiye da yadda ta ke yi zuwa yanzu.
Shugaba Donald Trump ya sha kokarin sa gwamnatocin jihohi da masana’antu su bude harkokin tattalin arzikinsu.
Amma kadan daga cikin gwamnoni 50 na kasar ne suka ba da umurnin yin hakan a ‘yan kwanakin nan.