Ganin yadda al’amura a fannoni da dama suka yi zafi a ‘yan shekarun nan a kasar wacce a baya ake sakawa a jerin mafi karfin tattalin arziki a yankin Afirka ta Yamma, suke nuna damuwarsu.
Babban zaben na Ghana abu ne da ‘yan kasar mazauna ketare ke dauka da muhimmancin gaske a bisa la’akari da tarin matsalolin da suka ce sun addabi kasar da al’ummarta kamar yadda wasu ‘yan Ghana mazauna Nijar suka zayyana wasu daga cikinsu wa Muryar Amurka.
Koda yake a cewarsu dukkan matsalolin da Ghana ke fuskanta a halin yanzu na tarnaki ga tafiyar lamuran jama’a ‘yan kasar mazauna jamhuriyar Nijar sun bukaci sabuwar gwamnatin da za ta karbi ragama bayan zabe ta fi ba da fifiko wa wadanan batutuwa.
Haka ita al’ummar ta Ghana na da rawar takawa don ganin komai ya gudana salun-alun a lokacin gudanar da zabe da bayan zabe mafarin wannan kira.
Ghana na daga cikin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a Afirka ta Yamma, yankin da ke fama da matsalolin tsaro, illolin canjin yanayi da koma bayan tattalin arziki, saboda haka yanayin siyasar kasar ta Ghana abu ne da ka iya shafar tafiyar harkoki a kasashen yankin.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barm:
Your browser doesn’t support HTML5