A shirin mu na matasa da siyasa a wannan mako, ganin cewar kwanaki kalilan kenan da aka gudanar da zabukan shugaban kasa da 'yan majalisu, a don haka ne dandalin VOA ya samu bakunci wani masani dangane da yadda suka nazarci zaben da aka gudanar.
Dr Sani Lawal Manumfashi malami a tsangayar kimiyyar Siyasa da ke jami’ar Bayero ta kano, na yadda ya nazarci yadda zaben da aka gudanar ya wakana a makon da ya gabata, inda ya ke cewa an samu karanci fitowa filin zabe.
Ya ce hakan na nuni da rashin gamsuwa daga bangaren alumma na yadda ake gudanar da harkokin siyasa a kasar nan, sannan matsalar amfani da kudi a lokutan zabe ya taka muhimmiyar rawa a tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce an lura da matsalolin sayar da kur’un a filin zabe inda yake jan hankalin mutane da su gane cewar sayar da katin kuri’a sayar da yancin su ne ga dan siyasa sannan su sani cewar muddin suka amince suka sayar da ‘yancin su toh lallai wannan dan siyasa sai ya girbe abin da ya shuka.
Dr Sani ya na mai bayyana cewa yadda zaben ya gudana ya nuna cewar mutane basu gamsu da yadda ake tafiyar da kasar ba hakan ce ma ta sa da dama suka ki fitowa domin su kada kuri'unsu.
Your browser doesn’t support HTML5