Kamar yadda bincike ya tabbatar, da wuya a wayi gari ba tare da an tare hanya an yi fashi ba, duk da kokarin da jami'an tsaro ke cewa suna yi.
Mallam Muhammad Oska daya daga cikin matafiyan da suka fada tarkon ‘yan fashi a tsakanin Demsa da Ngurore, ya ce 'yan fashin sun tilasta masu kwantawa inda suka rabasu da dukiyoyinsu.
Akwai wata mata ma da jaririnta sai da suka sata ta zauna kan jaririn idan ba haka ba kuma suka ce za su harbeta.
Kamar matafiyan, su ma ‘yan kasuwa sun ce abun takaici ne cewa yayin da jami’an tsaro ke tatsar kudadensu, akan hanya, har yanzu ba su tsira ba daga ‘yan fashi da makami musamman a jihohin Adamawa da Taraba.
Alhaji Ibrahim Muhammad mai shekaru 86, mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta Najeriya, Mai kula da jihohin arewa 19, ya bayyana halin da suke ciki a yanzu ya ce babu makon da ba'a tare 'yan uwansu akan hanya musamman ranar kasuwa a karbe duka kudadensu.
Saboda haka ya gargadi 'yan kasuwan da su daina tafiyar dare tare da kiran jami'an tsaro da su taimaka da kara jami'ansu akan hanyoyin musamman a Yola da Mubi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Othman Abubakar, ya ce suna daukan matakai tare kuma da musanta cewa suna shakulatin bangaro game da lamarin.
A farkon makwan nan ne ma tawagar babban hafsan sojin Najeriya ta ci karo da wani gungun ‘yan fashi da makami a hanyar zuwa Gombe, kuma tuni sojojin suka damke wadannan ‘yan fashin suka mikasu ga 'yan sanda.
Domin jin karin bayani saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz:
Your browser doesn’t support HTML5