Wata gobarar da ta tashi a wani otel dake a yankin Kurdawa na Arewacin Iraki ta hallaka mutane 30---wadanda suka hada da ‘yan Irakin da kuma ‘yan kasashen waje.
Wata gobarar da ta tashi a wani otel a yankin Kurdawa na Arewacin Iraki ta hallaka mutane 30---wadanda suka hada da ‘yan kasar ta Irak da kuma ‘yan kasashen waje kamar Canada, Sri Lanka, Bangladesh da Ingila. A kalla kuma mutane 23 ne suka sami raunuka a wannan gobarar da ta tashi da dare a birnin Sulaimaniyya. Wasu jami’an gwamnati a yankin sun ce da alamar dai tangardar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.