Fasahar Zamani Za Ta Kawo Ci gaba Da Ayukan Yi Ga ‘Yan Kasa -Emefiele.

CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele, ya ce tsarin tattalin arzikin fasahar zamani na da muhimmanci matuka, a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na kawo ci gaba a dukan fannoni a cikin shekaru masu zuwa.

Emefiele ya bayyana cewa, a yayin da ake samun karuwar yadda al’umma ke rungumar fasahar zamani hannu bi-biyu, ya zama wajibi gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su nemo hanyoyin da zasu yi amfani da tsarin fasahar zamani wajen inganta yanayin samun kudadden shiga.

Haka kuma akwai bukatar samar da hanyar da ‘yan Najeriya za su rika samun rance don bunkasa kasuwanci da ma tattalin arzikin kasar.

Gwamna Emefiele ya bayyana hakan ne a yayin bude taron karawa juna sani ga ‘yan jarida da ke aiki a bangaren hada-hadar kudi, kasuwanci da cinikayya da babban bankin na CBN ke shiryawa karo na 30, da aka gudanar lokaci daya a biranen tarayya Abuja da Ikko.

Taken taron na bana shi ne: “Amfani da damar tattalin arzikin fasahar zamani wajen bunkasa tattalin arziki, kawo cigaba mai dorewa da kuma samar da guraben aikin yi a yayin da duniya ke fama da annobar korona birus."

Emefiele ya kara da cewa, babban bankin Najeriya ya raba kudadde da suka kai naira bilyan 149 da milyan 210 ga 'yan kasar har dubu 316,869 da suka ci gajiyar shirin a karkashin karamin bankin NIRSAL, a wani mataki na saukaka wahalhalun da iyalai da masu kanana da matsakaitan sana’o’i suka yi ta fuskanta, don kawo ci gaba a lokacin da annobar korona birus ta yi kamari.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Kudadden da babban bankin ya rarraba wani sashe ne na naira bilyan 150 da bankin ya ware musamman ga iyalai da masu kanana da matsakaitan sana’o’i da bullar annobar korona birus ta yiwa mummunan tasiri.

Haka kuma ya ce, Najeriya na bukatar ingantattun hanyoyin fasahar zamani wajen bunkasa ci gaban tattalin arziki ‘yan kasar.

Emefiele wanda ya samu wakilcin mataimakinsa a bangaren ayyuka na babban bankin na Najeriya, Mr. Edward Adamu, ya lura cewa daya daga cikin fa'idodin da fasahar zamani ke haifarwa, shi ne yanayin sarrafa lokaci da wuri ta hanyar samar da intanet wanda ke hada hancin mutane daga kasashen daban-daban a fadin duniya.

Ya ce Najeriya na bukatar gina tattalin arzikin fasahar zamani mai karfi domin bunkasa tattalin arzikinta, musamman ma ta hanyar mai da hankali kan inganta kayan aiki na zamani, mafi kamar inganta tsarin samun Intanet, bukasa ayukan karatu da fasahar zamani, ayukan hada-hadar kudi na fasahar zamani, dandamali na zamani, da kuma kasuwanci na fasahar zamani.

Gwamnan babban bankin ya ci gaba da cewa a matsayin Najeriya na kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka kuma daya daga cikin mafi yawan matasa a duniya, tana da duk damar samun tattalin arzikin fasahar zamani mai karfi.

Ya jadada bukatar mayar da hankali wajen gina kakkarfan tubali biyar na tattalin arziƙin fasahar zamani da suka hada da kayan aikin zamani, dandamalin fasahar zamani, tsarin kuɗi na fasahar zamani, kasuwancin zamani da kuma koyar da sana’o'in hannu ta hanyar fasahar zamani.