Farin Jinin Trump Raguwa Yake Yi Ko Akasin Haka?

Shugaban Amurka Donald Trump

Yayin da adadin masu mutuwa sanadiyyar cutar coronavirus ke ci gaba da karuwa a Amurka, rahotanni na nuni da cewa, farin jinin shugaba Donald Trump na raguwa.

Ya zuwa wuraren karshen watan Maris, a lokacin da adadin mace-macen bai yi yawa ba, farin jinin Trump ya kasu zuwa kusan rabi inda adadin wadanda ba su gamsu da salon mulkinsa ba ya kai kashi 50.2 yayin da wadanda suka yi na’am da mulkin nasa adadinsu ya kai kashi 46.3 cikin 100, kamar yadda binciken jin ra’ayoyin jama’a da shafin da ake kira fivethirtyeight.com ya tattara.

To amma tun daga wannan lokaci, gibin ma’aunin salon mulkinsa ya fadada yayin da rahotannin yadda annobar corona take mamaye kasar, a gefe guda kuma shugaba Trump yake gudanar da taron manema labarai a kullum domin fadawa Amurkawa matakan da suke dauka wajen yaki da cutar.

Kawo yanzu, adadin wadanda cutar ta kashe a Amurka ya haura dubu 47.

A kuma halin da ake ciki, kashi 52.5 ne ba su gamsu da salon mulkin nasa ba yayin da kashi 43.5 suka nuna akasin haka, a cewar shafin yanar gizon na fivethirtyeight

Cikin kwanaki tara da suka gabata, binciken jin ra’ayin jama’a 24 cikin 25 da aka yi, sun nuna karbuwar shugaba Trump na fuskantar tawaya.

Sai dai wani shafin yanar gizo da ake kira realclearpolitics.com, ya nuna Shugaba Trump ya samu sakamako mai kyau wanda ya dan saba na shafin fivethirtyeight, inda ya nuna cewa kashi 51.5 ne ba su gamsu da salon mulkin Trump ba idan aka kwatanta da kashi 46 da suka nuna gamsuwarsu.