A jihar Imo a Najeriya, mutane sun fito da sanyin safiyar yau don a fara tantancesu daga baya kuma su fara kada kuri’arsu. Sannan kuma nan ma a Imo din zaben raba gardama ne da aka sami tarnaki a zaben gwamnonin da ya gabata na ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2015.
Sai dai a garin Nditoli jami’an tsaro sun yi awon gaba da wasu matsa da suka so yin amfani da maganar tangardar na’urar tantance masu kada kuri’a. Suna fara hatsaniyar ne kafin wakilin Muryar Amurka ya karasa wajen tuni jami’an tsaro sun yi awon gaba da su.
Haka kuma wakilinmu Lamido Abubakar Sokoto ya tabbatar mana da cewa a jihar Abia ma zaben na tafiya kamar yadda ya kamata. An yi rade-radin cewa akwai wani dauki ba dadi a garin, to da ya tuntubi kakakin ‘yan sandan jihar ta Abia ya tabbatar masa da cewa su komai yana tafiya lafiya lau.
Your browser doesn’t support HTML5