Farfesa Yemi Osinbajo Ya Ce Najeriya Ta Samu Rarar Naira Tiriliyon Guda Da Biliyan Dari Hudu

Jiya a jihar Kano mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci rufe taron yini uku na majalisar kula da tsare tsaren tattalin arzikin kasar wanda ma’aikatar kula da tsare tsaren ci gaban kasa bisa hadin gwiwa da gwamnatin Kano suka shirya.

Da yake gabatar da jawabi, Farfesa Osinbajo yace Najeriya ta samu rarar naira Tiriliyon guda da biliyan dari hudu daga cire tallafin mai zuwa yanzu.

Taron ya mayar da hankali ne wajan tattaunawa akan dabaru da kuma hanyoyin da za’a bi domin samun ci gaba mai dorewa da kasashen duniya suka rattabawa hannu a wannan shekara karkashin majalisar dinkin duniya.

Daftarin shirin mai kunshe da kudurori goma sha bakwai da suka hada da yaki da fatara, da samar da kyakkyawan muhalli, da kiwon lafiya, da shugabanci na gari da kuma wanzar da zaman lafiya da tsaro, na zaman ci gaba na aiwatar da shirin MDG, da yazo karshe a bana.

A wajan rufe taron, farfesa Osinbajo ya bayyana cewa wasu daga cikin kudurorin ci gaba mai dorewa sun dace da wasu tsare tsaren gwamnatin Najeriya na farfado da walwala da tada komadar tattalin arzikin kasar.

Domin Karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Farfesa Yemi Osinbajo Ya Ce Najeriya Ta Samu Rarar Naira Tiriliyon Guda Da Biliyan Dari Hudu