Kamar yadda ake sa ran gudanar da sallar ne a farkon makon gobe, sai dai kuma sallar na zuwa ne cikin wani halin tashin gwauron zabi da Raguna sukayi a bana. Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, ya ziyarci babbar kasuwar garin Jimeta inda ya shaida karancin masu sayan ragunan.
A cewar sarkin Tike Alhaji Mohammad Yalo, wanda shine mataimakin shugaban kungiyar fataken dabbobi na Jimeta, yace hasashe na nuna musu cewa bana akwai karancin Raguna domin yanzu haka akan sayesu ne domin fitar da su kasar Kamaru. Alhaji Mohammad yayi kira ga jama’a da cewa duk mai niya ya hanzarta ya sayi nasa ragon da wuri.
Yayin da matsalar rayuwa ke kara yawa a wasu sassan Najeriya, kamar yadda rahotanni ke cewa wasu ‘yan baranda suka fara shiga wasu ‘kauyuka suna saye amfanin gonar da aka noma, abin da yasa wasu magidanta ke kokawa.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5