Kamar yadda ya rage saura mako guda ayi a fara bukin karamar sallah, hada hada ta kara kankama a kasuwanni inda mutane ke zuwa domin sayan kayayyakin sallah.
A kasuwar Kantin Kwari ma hakan abin ya ke domin kasuwar ta cika makil kamar yadda aka saba gani a baya, sai dai mutane na korafin cewar kaya sun yi tsada sosai.
Wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir, ta zanta da wani mutum da yaje sayayya kasuwar, inda ya shaida mata cewa ya taho tun daga Abuja don yana ganin zai fi samun saukin kayayyaki a kasuwar Kano, amma sai gashi hakan bata faru ba.
Haka zalika sauran masu sayayya a wannan kasuwa na ta korafi kan tsadar kaya da suke fuskanta. A daya bangaren kuma wani dan kasuwa ya koka ga rashin kudade a hannun masu sayen kaya, ya kuma nuna cewa ba ‘yan kasuwar bane ke kara kayayyaki, kamfanonin dake raba musu kayan ne ke kara musu kudu.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5