A tattaunawar da muka yi da wasu mata, wata uwa da ta nemi a sakaya sunanta ta ce tuni ta gama sayen kayyakin da take bukata kamar robar adana abinci domin murnar zuwan watan Ramadan, ta ce ta sayi kofukan shan ruwa da sauran su, kuma tana kokarin sayen kayan miya kuma ta ce farashin ba laifi.
Haka ma wata magidanciya ta bayyana cewa farashin kayan masarufi a wannan shekara bai hau kamar na shekarar data gabata ba, kuma suna fatan kasuwar ta dore a hakan.
Malam Khamalidun Ikara, magidanci da muka gana da shi a wanna kasuwa, ya bayyana cewa farashin yana nan bai tashi ba tukunna, ya kuma kara da cewa yana fatan farashin ya tsaya a yadda yake.
Daga nan kuma mun tuntubi 'yan kasuwa a nasu bangaren ko sun rage farashin kayayyakin nasu ko akasin haka – duk kuwa da cewar tuni wasu mata suka fara tanajin kayayyakin kwalliya da wuri-wuri kafin sallah ta karato.
Alhaji Ahmad, ya ce ba kamar shekarar da ta gabata ba a bana kaya sun yi sauki sai dai kasuwar babu mutane sosai sakamakon rashin isassun kudi a hannun mutane.
Malamai dai na ta kokarin jan hankali 'yan kasuwa da su yi sassauci a wannan wata domin samun dinbim lada.
Domin cikakken bayani saurari hirar a nan.
Your browser doesn’t support HTML5