Farashin Jarin Kamfanin IntelliPharmaceutics Yayi Sama Bayan Da Dr. Isa Odidi Ya Bude Kasuwar NASDAQ

Dr. Isa Odidi a kasuwar NASDAQ jim kadan kafin ya kada kararrawar bude kasuwar, dake New York, Jumma'a, 22 Oktoba, 2010

Kasuwar hada-hadar hannayen jarin kamfanonin fasaha, NASDAQ, ta karrama masanin kimiyyar sarrafa magungunan dan Najeriya da kamfaninsa na IntelliPharmaceutics

Jim kadan a bayan da ya kada kararrawa ta bude kasuwar NASDAQ ta hada-hadar hannayen jarin kamfanonin fasaha yau jumma'a a nan birnin New York, Dr. Isa Oddi da mai dakinsa Dr. Amina Odidi, sun daga kai suka kalli yadda farashin hannun jari na kamfaninsu mai suna IntelliPharmaceutics ya rika cirawa sama.

Kasa da minti 10 a bayan da kasuwar ta NASDAQ ta karrama Dr. Isa Odidi, farashin hannun jarin kamfanin ya tashi da kimanin kashi 3 cikin 100. Wannan shi ne karon farko da kasuwar NASDAQ, wadda ta kunshi manyan kamfanonin fasaha na duniya irinsu Microsoft, ta karrama wani dan asalin Najeriya ta hanyar gayyatarsa ya bude wannan kasuwar.

Haka kuma, wannan karramawa ta zo shekara guda cif a bayan da kamfanin sarrafa magungunan na IntelliPharmaceutics ya fara sayar da hannayen jarinsa a kasuwar ta NASDAQ.

A cikin jawabinsa na bude kasuwar, Dr. Odidi ya bayyana cewa shi wannan kamfani na su ya kware ne wajen sarrafa wasu nau'in magungunan da za a iya kayyade lokacin da zasu fara aiki a jiki, abinda yana iya kara kaifin wannan magani. Ita wannan fasahar ana iya amfani da ita a kan sabbin magunguna da ma magungunan da ake da su a yanzu.

Manyan darektoci, da wakilan hukumar zartaswar kamfanin IntelliPharmaceutics da masu zuba jari da kuma baki daga Najeriya, kamar Dr. Abdu Mukhtar Dambatta na kamfanin zuba jarin da ake kira Abuja Investments Company, suka halarci wannan bukin a hedkwatar kasuwar ta NASDAQ dake dandalin Times Square a nan New York.