Hukumomin Najeriya sun kama dan'uwan tsohon madugun tsagera Henry Okah, bisa zargin cewa shi ma da hannunsa a tagwayen hare-haren bam na mota da suka kashe mutane 12 a Abuja.
Wata majiyar tsaro ta fadawa 'yan jarida jiya lahadi cewa an kama Charles Okah a Lagos, aka tafi da shi Abuja. Suka ce ana zargin ya samar da kudin kai hare-haren na ranar 1 ga watan Oktoba.
Har ila yau majiyar ta zargi Charles Okah da laifin aikewa da sakonnin Email a madadin kungiyar tsagera ta MEND, wadda ta dauki alhakin kai hare-haren. Sakonnin Email da kungiyar MEND ke aikawa a koyaushe tana dauke da sunan Jomo Gbomo ne, kuma daga adireshi na Yahoo ake aikawa.
AS farkon wannan wata aka kama Henry Okah a Afirka ta Kudu, aka tuhume shi da aikata ta'addanci bisa zargin cewa shi ne ya kitsa kai hare-haren na bam. Okah, wanda aka yi imanin cewa shi ne tsohon madugun kungiyar MEND, ya musanta cewa da hannunsa a wannan lamarin.
Hukumomin Najeriya sun tsare wasu mutanen su tara dangane da wadannan hare-hare.