Farashin damar nuna wasannin gasar Bundesliga ta kasar Jamus a gidajen talabijin zai sauka a tsakanin shekarar 2021 da 2015, daga Yuro biliyan 1.16 zuwa biliyan 1.1 a kowace kakar wasanni, a cewar shugaban gasannin league na kasar Jamus, Christian Seifert a yau Litinin.
Adadin farashin da zai kama Yuro biliyan 4.4, shi ne karon farko da ya fadi kasa tun daga shekara ta 2002, sa’adda aka yi matsaya akan farashin, haka kuma ba ko daya daga cikin masu ruwa da tsaki a sha’anin yada wasanni a talabijin a halin yanzu.
Seifert ya bayyana cewa kwantaragin za ta shata wani sabon tsari na farashin nuna wasanni, bayan annobar COVID-19.
To sai dai ya bayyana sabon tsarin da cewa ya na da inganci da sahihanci, idan aka kwatanta shi da tayin farashin da aka yi wa sauran manyan gasannin kwallon kafa na nahiyar Turai.
Gasar Bundesliga ta kasar Jamus ita ce ta farko da aka sake dawowa a Turai tun a cikin watan Mayu, bayan da aka dakatar da dukkan lamurran wasanni a fadin duniya sakamakon annobar coronavirus.