Faransawa Na Ci Gaba Da Jimamin Wadanda Suka Mutu Ko Suka Ji rauni
Ma'aiukatan agaji su na duba mutanen da aka kashe ko aka ji musu rauni a kofar wani gidan abinci a Paris.
'Yan sanda su na yin sintiri a gundumar nan ta Place de la Republique dake birnin Paris asabar, kwana guda a bayan wasu munanan hare-haren da suka kashe mutane fiye da 100.
Sojojin Faransa su na yin sintiri a kusa da hasumiyar nan ta Eiffel Tower, kwana guda a bayan munanan hare-hare a birnin Paris.
Wasu daga cikin wadanda suka kubuta da rayukansu a dakin wasa na Bataclan dake Paris a daren Jumma'a 13 Nuwamba, 2015.
Shugaba Francois Hollande yana jawabi ga al'ummar Faransa a bayan hare-haren ta'addancin da kungiyar ISI ta ce ita ce ta kai a daren jumma'a 13 Nuwamba, 2015. Shugaban ya ce duk mai hannu a wadannan hare-haren zai gwammace kida da rawa.
Wani mutumi ya rike kai a lokacin da yake ajiye furanni na jimami a kofar wani gidan abinci mai suna Carillon cafe, a Paris, Nov.14, 2015.
Taswirar wuraren da aka kai ma hare-hare a birnin Paris.
Wasu 'yan jarida su na aiki a kofar wani gidan abinci inda ake iya ganin yadda harsashi ya huda gilashin kofar a Paris.
Mutane su na wucewa ta jikin farfajiyar da aka killace ta gidan wasa na Bataclan, kwana guda a bayan mummunan harin da ya kashe mutane da yawa cikin dakin wasan dake Paris.
'Yan sandan Faransa su na binciken motoci a bakin iyakar kasar da Italiya, kusa da La Turbie, asabar 14 Nuwamba, 2015.