Faransa Ta Fice A Gasar Cin Kofin Duniya Ta ‘Yan Kasa Da Shekaru 20

Gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20

A halin da ake ciki, Ingila ta samu darewa matsayi na farko a rukunin E bayan da ta tashi canjaras da Iraqi.

Tawagar ‘yan wasan Faransa ta fice daga gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 duk da doke Honduras da ci 3-1.

Faransa ta sha kaye a wasanninta biyu na farko a rukunin G, lamarin da ya ba Gambia da Koriya ta Kudu damar yi mata fintinkau.

Faransa ta so ta samu karin kwallo daya akan ukun da ta zurawa Honduras, sai dai hakan ya ci tura.

Da a ce ta zura kwallaye hudu, da ta karbe gurbin Tunisia cikin fitattu hudu a zagayen na 16, amma hakan ya ci tura.

A halin da ake ciki, Ingila ta samu darewa matsayi na farko a rukunin E bayan da ta tashi canjaras da Iraqi.

Uruguay ta zo ta biyu bayan da ta doke Tunisia da ci 1-0, ko da yake, Tunisian ta samu tsallaka wa zagaye na gaba.