Wannan shawarar ta zo ne bayan da wani babban sojan kasar Assimi Goita, wanda ya jagoranci juyin mulkin bara, ya kori shugaban rikon kwarya na kasar da Firayim Ministan kasar a makon da ya gabata.
Wannan matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a diflomasiyya, lamarin da ya sa Amurkan ta dakatar da bayar da taimakon tsaro ga jami'an tsaron na Mali da kuma Kungiyar Tarayyar Afirka da Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) su dakatar da Mali.
Sojojin kasar Faransa sun fada jiya Alhamis cewa "ECOWAS da kungiyar Tarayyar Afirka sun tsara lamuran da kuma jan layi domin fayyace tsarin sauyin siyasa a Mali."
"Yayin jiran wadannan garanti, Faransa ta yanke shawarar dakatar, a matsayin wani matakin wucin gadi, ayyukan hadin gwiwa na soji tare da sojojin Mali da kuma shawarwarin kasa don amfanin su," in ji ma'aikatar a cikin wata sanarwa da AFP ta gani.
Saurari wani karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5